Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (2024)

Duk mutumin da ya lashe zaben Kenya a ranar 9 ga watan Agusta zai fuskanci tarin matsalolin siyasa da na tattalin arziki da sauransu.

A wadannan taswirori mun yi bayani kan wasu daga cikin abubuwan da ke zuciyar masu kaɗa kuri’a yayin da za su fita rumfunan zaɓe.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (1)

Dole mutumin da zai zama sabon shugaban kasa ya bijiro da hanyoyin taimakawa mutane iya samun kayayyakin bukatun yau da kullum.

‘Yan Kenya, kamar a sauran ƙasashe, sun fahimci cewa kudadensu sun rage daraja don haka ba sa iya sayayyar abubuwan amfanin yau da kullum.

A watan Yuni, an samu hauhawar farashi da kashi 7.9 cikin 100, sai dai an fi samun karin kan wasu muhimman kayan masurufi da abinci, ciki har da garin masara da man girki.

Domin samar da rangwame, gwamnati mai barin gado ta Shugaba Uhuru Kenyatta ta rage farashin garin masara a watan Yuli, sai dai babu tabbacin ko wannan tsari zai ɗore.

Matsalar fari na shafar al’ummar Kenya miliyan uku, lamarin da ya sa mutane da dama ke fafutikar ganin yadda za su samu abinci.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (2)

Gwamnatin tana kuma bayar da tallafi a fannin man fetur domin sama wa al’umma sauki.

Amma wannan tsari na zuwa da nasa asarar ta kusan dala miliyan 141 a watan Yuli – wanda ke zama wani ƙarin bashi kan basussukan da suka shake wuyan kasar.

Ana samun wannan ƙaruwa a karkashin gwamnatin Mista Kenyatta, kuma ana ganin tasirinta a karin kashi 68 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikin kasa na GDP.

  • Yadda tabar wiwi da dafin macizai suka kara wa yakin neman zaben Kenya armashi
  • Shugaban kasar da ba ya so mataimakinsa ya gaje shi

Gwamnatin ta karbi rancen kudade domin gudanar da manyan ayyuka kamar layin-dogo da China ke shimfidawa domin hade birnin Nairobi da yankunan gabar teku.

Zuba hannayen jari a fannin gine-gine na iya taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki na dogon-zango, sai dai abubuwan da hakan zai kusan da dama – gina layin-dogo ya kunshi dala biliyan 3.2.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (3)

Sama da kashi daya cikin uku na al’ummar Kenya ba su haura shekara 35 ba, kuma su ne suka fi yawa wajen jefa kuri’a.

Shawo kan matsalolin matasa na iya taimakawa sosai waje nasara a zabe.

Galibin matasa ‘yan shekara 18 zuwa 35 ba su da aiki duk da digirinsu da wasu shaidar karatu masu muhimmanci.

Galibin matasan da shekarunsu suka soma daga 18 na ganin cewa akwai bukatar bai wa fannin ilimi fifiko.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (4)

A shekarun baya-bayan nan, Kenya ta yi nasara wajen bunkasa fannin Iliminta.

Gwamnati ta bijiro da tsarin ilimi kyauta ga ‘yan firamare a 2002, hakan ya bai wa yara masu yawa damar samun ilimi.

An samu karuwar yara da ake kai wa makarantun sakandare, wanda tun a 2008, ake ba da tallafi a karatun.

Sai dai duk da hakan, kashi daya bisa biyar na daliban sakandare a Kenya ba sa kammalawa.

Iyayen dalibai da dama sun gwammace su biya kudin makarantar ‘ya’yansu, a ganinsu hakan ne zai sama musu ilimi mai inganci, a makarantu masu zaman kansu.

Wani abu mai muhimmanci shi ne yadda mutane za su jefa kuri’a bisa kabilanci.

Akwai hasashen cewa manyan ‘yan takarar biyu, Raila Odinga da William Ruto, za su samu galibin kuri’unsu daga kabilar da suka fito.

Amma dai wannan shi ne karo na farko a zaben Kenya da manyan ‘yan takara ba su fito daga fanin kabila mafi girma ba, wato Kikuyu.

Dukkanin ‘yan takarar biyu sun fahimci haka shi ya sa suka zabi mataimaka daga bangaren Kikuyu.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (5)

Kenya na da karfin tattalin arziki a yankin gabas kuma duk abin da ya faru a kasar za a ga tasirinsa a gabashin Afirkan.

A shekarun baya-bayanan ta rasa bakin fada a Ethiopia, amma kuma idan ka kalli kudaden shigowar kowanne mutum mafi matsakaici a Kenya, ya na haura dala dubu biyu a shekara, ya rubanya na kasashe makwabtanta daga arewaci.

Sai dai, wadannan alkaluma, da aka kiyasta a shekarar da ta gabata, na nuna wagegen bambanci a ƙasar kuma ba lallai ya kunshi tasirin matakan kulle na lokacin annobar korona.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (6)

Mamayar wasu yankuna na Kenya na tasiri wajen yawan mutanen da ke da damar samun lantarki da intanet.

Alkaluman na nuna cewa kusan kashi uku cikin 10 na 'yan Kenya ba su da damar samun lantarki, sannan galibi ba su da intanet.

Inganta wannan fanni zai kasance zakaran gwajin dafi ga duk mutumin da ya lashe zaben.

Zaben Kenya na 2022: Taswirar da ke fayyace bayanai kan ƙasar - BBC News Hausa (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Duane Harber

Last Updated:

Views: 5835

Rating: 4 / 5 (51 voted)

Reviews: 82% of readers found this page helpful

Author information

Name: Duane Harber

Birthday: 1999-10-17

Address: Apt. 404 9899 Magnolia Roads, Port Royceville, ID 78186

Phone: +186911129794335

Job: Human Hospitality Planner

Hobby: Listening to music, Orienteering, Knapping, Dance, Mountain biking, Fishing, Pottery

Introduction: My name is Duane Harber, I am a modern, clever, handsome, fair, agreeable, inexpensive, beautiful person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.